30 Janairu 2021 - 13:27
Kasar Sin Ta Yi Fushi Da Shirin Kasar Burtaniya Na Bawa ‘Yan Yankin Hong-kong Takardun Zama ‘Yan Kasar Burtaniya

Gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa ba zata amince da sabon shirin kasar Burtaniya na bawa ‘yan yankin Hong kong na kasar ta Sin takardun zaman ‘yan kasar Burtaniya ba.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayya cewa a ranar Lahadi mai zuwa ne hukumar shige da fice ta kasar Burtaniya za ta bude shafin yanar gizo na karban takardun neman zama a kasar Burtaniya daga mutanen Hong Kong.

Firai ministan kasar ta Burtaniya Boris Jonson ya yi maraba da wannan shirin ya kuma bayyana cewa ‘yan yankin Hong Kong na kasar Sin kimani miliyon 3 ne, ake saran zasu amfana da wannan shirin.

Labarin ya kara da cewa, da farko za’a bawa ‘yan yankin na Hong kong da iyalansu izinin zama a kasasr na Burtaniya na tsawon shekaru 5, sannan daga baya suna da damar neman izinin zama ‘yan kasar.

Gwamnatin Burtaniya wacce ta yiwa yankin Hong kong mulkin mallaka na daruruwan shekaru ta dauki wannan matakin ne bayan da kasar Sin ta kafa wasu dokoki a yankin na Hong Kong wanda ya sabawa yarjejeniyar mika yanking a kasar Sin a shekara ta 1997. 

342/